Bakonmu a Yau
Kasar Ghana ta ayyana zaman makoki na mako guda kan mutuwar kofi Anan
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:31
Gwamnatin kasar Ghana na cikin zaman makoki na tsawon mako daya, domin girmama tsohon Sakatar- Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Anan, da ya mutu a ranar Asabar a wani asibiti dake Geneva a kasar Switzerland. Bayan share tsawon shekaru 80 na zaman duniyaMarigayi Kofi Anan ya kasance haifaffen kasar Ghana ne kuma ya jagoranci Majalisar Dinkin Duniya a tsakanin shekara ta 1997 zuwa 2006.Ambassador Shuaibou Sheriff dan siyasa ne a Ghana wanda ya sha muamulla da marigayin, ya yi wa Garba Aliyu Zariya bayyani kan rashin na marigayin.