Isa ga babban shafi

'Yan tawayen Afrika ta Tsakiya sun gindaya sharudda 97 kafin sulhu

Kungiyoyin da ke dauke da makamai a jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun gabatar wa kungiyar Tarayyar Afirka wani daftari da ke kunshe da muhimman bukatunsu kafin amincewa sun kwance damara da kuma samar da zaman lafiya a kasar.

Wasu mayakan kungiyar 'yan tawayen Seleka a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a sansaninsu dake kusa da garin Lioto. Daukar hoto, 9 ga Yuni, 2014.
Wasu mayakan kungiyar 'yan tawayen Seleka a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, a sansaninsu dake kusa da garin Lioto. Daukar hoto, 9 ga Yuni, 2014. REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

A cikin wannan kundi, kungiyoyin ‘yan tawayen sun gabatar da bukatu guda 97, da suka hada da yi masu afuwa ta bai-daya da kuma sake yi wa rundunar tsaron kasar garambawul matukar dai ana bukatar samun dauwamammen zaman lafiya a kasar.

A ranar litinin ta makon gobe ne wani babban jami’in kungiyar ta Tarayyar Afirka zai gana da wakilan kungiyoyin da suka gabatar da wadannan bukatu a gari Bouar da ke yammacin kasar, inda zai yi tattaunawar farko da su kafin gabatar da bukatun nasu ga hukumar kungiyar da ke kokarin samar da zaman lafiya a kasar.

Wasu daga cikin mayakan na bukatar janyewar dakarun Rasha daga kasar kafin su ajiye makamansu, sharadin da ake ganin cewa zai kasance mai wuya ya samu karbuwa daga gwamnatin birnin Bangui, wadda ke cigaba da samun kusanci da Rasha a ‘yan watannin baya-bayan nan.

Kungiyar Tarayyar Afirka na samun goyon bayan MDD a wannan yunkuri na samar da zaman lafiya, kuma tuni wakilan kwamiti na musamman da kungiyar ta kafa domin sulhunta rikicin kasar suka gana da tsaffin shugabannin kasar, Michel Djotadia da ke zaune a jamhuriyar Benin, da kuma Francois Bozize da ke zaune a Uganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.