Isa ga babban shafi
Mali

Har abada ba zan amince da zaben shugabancin Mali ba - Cisse

Dan takarar ‘yan adawa a zaben shugabancin Mali Soumaila Cisse, ya ce har abada ba zai taba amincewa da shan kaye a zaben da kotun tsarin mulki ta tabbatar da Ibrahim Boubacar Keita a matsayin wanda ya yi nasara ba.

Souma'ila Cisse dan takarar da ya sha kaye a zaben shugabancin Mali.
Souma'ila Cisse dan takarar da ya sha kaye a zaben shugabancin Mali. Michele CATTANI / AFP
Talla

A taron manema labaran da ya gabatar jiya alhamis a birnin Bamako, Cisse ya ce har yanzu yana nan kan bakansa na watsi da sakamakon zaben, inda ya ce alkaluman da kotun tsarin mulkin ta yi amfani da su, an tattara su ne ta hanyar magudi.

A ranar 12 ga watan agusta da muke ciki, aka gudanar da zaben shugabancin Mali zagaye na biyu, inda shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita ya lashe kashi 67.16 na yawan kuri’un da aka kada, yayinda Souma’ila Cisse ya samu kashi 32.84.

A baya bayan nan dai daruruwan magoya bayan Cisse sun gudanar da jerin zanga-zanga a birnin Bamako domin nuna adawa kan nasarar da Keita ya samu kan gwaninsu.

A ranar 4 ga watan Satumba mai zuwa ake sa ran rantsar da Ibrahim Boubacar Keita a wa’adi na biyu inda zai sake shafe tsawon shekaru 5 yana jagorancin kasar Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.