rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Senegal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kotun ta haramtawa Khalifa da Karim Wade shiga zabe

media
Khalifa Sall tsohon magajin garin Dakar a kotu RFI/Guillaume Thibault

Kotun Koli a kasar Senegal ta dakushe bukatar biyu daga cikin manyan yan takaran shugabancin kasar na kalubalantar shugaba Macky Sall a zaben shugaban kasa.

Kotun ta haramtawa Khalifa Sall da Karim Wade damar tsayawa zaben.


Shidai Khalifa Sall ya ruga kotu ne domin neman ganin ta soke hukuncin daurin shekaru 5 da aka masa saboda samun sa da laifin karkata kudaden hukuma lokacin da yake rike da mukamin magajin garin birnin Dakar, amma sai kotun taki, inda ta amince da daurin shekaru 5 da aka masa.

Dan tsohon shugaban kasar Karim Wade, yaje kotun ne domin ganin ta tilastawa hukumar zabe sanya sunan sa cikin yan takarar zaben shekara mai zuwa, amma kotun taki amincewa da bukatar.

Yan adawar guda biyu na da tarin magoya bayan da ake ganin zasu iya yiwa shugaba Sall barazana, yayin da lauyoyin su ke cewa gwamnati na amfani da kotunan ne wajen hana su tsayawa zaben.

A shekarar 2015 aka daure Wade shekaru 6 a gidan yari saboda samun sa da laifin azurta kan sa da kudaden gwamnati.