Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Adadin sojin Najeriya da suka mutu a harin Boko Haram ya tasamma 50

An gano karin gawarwakin dakarun sojin Najeriya 17 da suka rasa rayukansu yayin fafatawarsu da mayakan boko haram a arewacin Maiduguri gab da kan iyakar Najeriyar da Jamhuriyyar Nijar, a wani hari da suka kai musu na yunkurin kwace iko da sansaninsu da ke garin Zari.

Yanzu haka dai dakaru na musamman daga Bataliyar sojin Najeriyar ta 145 na ci gaba da aikin lalubo wadanda suka bace bayan harin yayinda su ke aikewa da gawarwakin da suka gano zuwa garin Maiduguri.
Yanzu haka dai dakaru na musamman daga Bataliyar sojin Najeriyar ta 145 na ci gaba da aikin lalubo wadanda suka bace bayan harin yayinda su ke aikewa da gawarwakin da suka gano zuwa garin Maiduguri. REUTERS/Tim Cocks
Talla

Jaridar Premium Times ta Najeriyar ta ruwaito yadda tawagar masu binciken gawarwakin sojin bayan rikicin na daren ranar Alhamis ta gano gawar wani Hafson soji guda da kuma kananan soji 16 cikin karshen makon nan a yankin karamar hukumar Mobbar.

Tun a daren ranar Alhamis ne wani adadi mai yawa na mayakan boko haram ya dirarwa sansanin sojin najeriyar da ke kauyen Zari gab da iyakar Nijar inda bayan fafatawa mayakan suka hallaka tarin jami’an baya ga jikkata wasu da dama.

Yanzu haka dai dakaru na musamman daga Bataliyar sojin Najeriyar ta 145 na ci gaba da aikin lalubo wadanda suka bace bayan harin yayinda su ke aikewa da gawarwakin da suka gano zuwa garin Maiduguri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.