Isa ga babban shafi
Kamaru-'Yan ware

Paul Biya ya caccaki matakin hana 'yan aware damar samun Ilmi

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya, ya yi kakkausar suka dangane da abin da ya kira tauye hakkin jama’a tare da hana su damar samun ilimi a yankin ‘yan arewa da ke amfani da turancin Ingilishi.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya.
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya. REUTERS/Mike Segar
Talla

Yin garkuwa da malamai ko shugabannin makarantu, wani lokaci har ma da kashe su, na daga cikin matsalolin da ake fuskanta, lamarin da ke cigaba da kawo cikas matuka ga bangaren ilimi a yankin na ‘yan aware.

Kafin kammala hutun karshen shekara da kuma sake bude makarantu a farkon wannan mako, gwamnatin kasar ta yi alkawarin samar da tsaro da kuma kariya ga malamai da sauran ma’aikatan ilimi, to sai dai ga alama har yanzu malaman da kuma shugabannin makarantu na fuskantar barazana daga ‘yan bindiga.

Bara warhaka ne rikici ya sake barkewa a yankin, inda shugabannin masu gwagwarmayar ke nuna rashin amincewa da abinda suka kira tilasta wa jama’a rungumar tsarin koyarwa na Faransanci a maimaikon Ingilishi, lamarin da ya haifar da koma-baya matuka ga sha’anin ilimi a yankin.

Daga bisani dai ‘yan bindiga sun cigaba da kai hare-hare ba wai a kan malaman makarantu kawai ba har ma da sauran jami’an gwmanati, to sai dai duk da cewa an tura dimbin jami’an tsaro domin murkushe masu boren har yanzu lamarin sai kara tabarbarewa ya ke yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.