rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Eritrea Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An bude iyakokin Eritrea da Habasha bayan shekaru 20 a kulle

media
Firaminista Abiy Ahmed da takwaransa Isaias Afwerki yayin sanya hannu kan wata sanarwa da ke kawo karshen takaddamar da ke tsakaninsu ranar 9 ga watan Yulin 2018. Twitter/Yemane G. Meskel

Kasashen Habasha da Eritrea sun sanar da bude iyakokinsu ta kasa a hukumance karon farko cikin shekaru 20, matakin da ke nuna ci gaba da daidaituwar alaka tsakaninsu a baya-bayan nan.


Ma'aikatar yada labaran Eritrea ta ce Firaminista Abiy Ahmed da kansa ya halarci taron bude kan iyakokin bayan kasancewarsu a rufe tsawon shekaru sakamakon tsamin alakar da ke tsakaninsu.

Iyakokin da aka gudanar da bikin budewar ta su sun hadar da na Gabashin kasar da na yammaci wadanda aka kullesu a shekarar 1998 bayan yanke huldar Diflomasiyya tsakanin kasashen na Eritrea da Habasha sakamakon yakin shekaru 2 da suka shafe suna tafkawa.

Bude iyakokin na daga cikin matakan baya bayan nan da shugabannin kasashen biyu ke dauka wajen ganin sun kawo karshen rashin fahimtar da ke tsakaninsu.