Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Jam'iyyar MDC za ta rantsar da Chamisa a shugaban Zimbabwe

Babbar Jam'iyyar adawa ta MDC a Zimbabwe ta sha alwashin rantsar da Dan takarar shugabancin kasar da ya sha kaye a zaben watan Yuli Nelson Chamisa a matsayin halastaccen shugaban kasa cikin makon nan bayan da ta yi zargin cewa an juyar da sakamakon zaben ne wanda ya nuna shi ke da nasara.

Jam'iyyar ta MDC ta ce za ta rantsar da Chamisa a ranar asabar ta makon nan yayin bikin cikarta shekaru 19 da kafuwa.
Jam'iyyar ta MDC ta ce za ta rantsar da Chamisa a ranar asabar ta makon nan yayin bikin cikarta shekaru 19 da kafuwa. REUTERS/Mike Hutchings
Talla

Zaben wanda shi ne karon farko da Zimbabwe ta gudanar tun bayan dogon mulkin shugaba Robert Mugabe da ya share kusan shekaru 40 yana kan karagar mulki kafin murabus dinsa a watan Nuwamban bara, Nelson Chamisa ya yi zargin hadin baki tsakanin hukumar zabe da shugaban kasar Emmerson Mnangagwa wajen murde sakamakon zaben.

Chamisa wanda shi ke jagorantar babbar jam'iyyar adawa ta MDC a Zimbabwe ya shigar da kara kan dakatar da rantsar da Mnangagwa amma kuma kotun kundin tsarin mulki ta yi watsi da karar sakamakon rashin hujjoji.

Jam'iyyar ta MDC ta ce za ta rantsar da Chamisa a ranar asabar ta makon nan yayin bikin cikarta shekaru 19 da kafuwa.

Sakamakon zaben na Zimbabwe dai ya nuna Mnangagwa ke jagoranci da akalla kuri'u kashi 50.8 yayinda Chamisa ke biye masa baya da kashi 44.3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.