Isa ga babban shafi
Zimbabwe

An fasa rantsar da Chamisa a matsayin shugaban kasa

Jam’iyyar MDC mai adawa a Zimbabwe ta soke taron da ta shirya gudanarwa don rantsar da jagoranta, Nelson Chamisa a matsayin shugaban kasa bayan gwamnati ta hana gudanar da taron jama’a a birnin Harare sakamakon barkewar annubar cutar Kwalara.

Jagoraan 'yan adawar Zimbabwe Nelson Chamisa
Jagoraan 'yan adawar Zimbabwe Nelson Chamisa REUTERS/Mike Hutchings
Talla

MDC ta shirya taron ne don jaddada ikirarinta na cewa, an tafka magudi a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 30 ga watan Juli, in da ta ce, Chamisa ne halastaccen shugaban kasa a maimakon Emmerson Mnangagwa na jam’iyyar ZANU-PF mai mulki.

MDC ta zargi gwamnati da fakewa da annubar Kwalara da ta kashe mutane 25 don hana ta gudanar da bikin rantsuwar wanda ya zo dai dai da cikar jam’iyyar shekaru 19 da kafuwa.

Mai magana da yawun ta MDC, Jacob Mafume ya ce, jam’iyyar ta dage bikin da ta shirya gudanarwa, in da ya ce matakin da gwamnati ta fake da shi ba shi gamsarwa.

A farkon wannan watan ne, aka fara gano barkewar Kwalarar a garin Glen View da ke wajen birnin Harare, in da akalla mutane dubu 3 suka kamu da ita, lamarin da ya sa hukumomin lafiya suka ayyana dokar ta baci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.