Isa ga babban shafi
Kamaru

Gwamnati ta hana 'yan Kamaru tserewa daga gidajensu

Mahukuntan Kamaru sun haramta wa mazauna yankunan’yan aware da ke fama da rikici tserewa daga gidajensu, yayin da ya rage kasa da makwanni uku a gudanar da zaben shugaban kasar.

Jami'an tsaro a yankin Buéa na Kamaru.
Jami'an tsaro a yankin Buéa na Kamaru. AFP/Alexis Huguet
Talla

Kungiyoyin agaji a birnin Buweya fadar gwamnatin lardin kudu maso yammacin kasar da ake kallo a matsayin babbar cibiyar ‘yan aware, sun ce, ko a karshen makon da ya gabata, daruruwan iyalai ne suka tsere daga yankin sakamakon tsanantar tashe-tashen hankula.

To sai dai a wata hira da aka watsa a gidan talabijin mallakin gwamnatin kasar, gwamnan lardin Okalia Bilai, ya ce ba za a hana jama’a yin balaguro daga yankin zuwa sauran sassa na kasar ba, amma an haramta duk wani yunkuri na kwashe iyalai domin barin yankin

Gwamnan ya sanar da haka ne bayan da ya ziyarci babbar tashar mota da ke birnin na Buweya, in da ya tarar da daruruwan mutane dauke da kayayyakinsu na barin garin zuwa birnin Douala da sauran birane da ke tsakiyar kasar.

Rahotanni sun ce, jama’a na barin yankin ne sakamakon bayanan da ke cewa yanzu haka dakarun gwamnati na shirin kaddamar da wani gagarumin farmaki kan ‘yan aware, wadanda tuni gwamnatin ta bayyana su a matsayin ‘yan ta’adda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.