rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Liberia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana zargin mutane 15 da handame milyoyin kudade a Liberia

media
Zababben shugaban Liberia, George Weah na zantawa da Reuters a gidansa da ke Monrovia, Liberia, 2 ga watan janairun2018ERS/Thierry Gouegnon REUTERS/Thierry Gouegnon

Gwamnatin Liberia ta hana wa wasu mutane 15 ficewar daga kasar ciki har da dan tsohuwar shugaba Ellen Johnson Sirleaf, a cigaba da bincike dangane da bacewar wasu kudaden da yawansu ya kai dalar Amurka milyan 104 mallakin kasar.


Rahotanni sun ce wadannan kudade ne da babban bankin kasar ya sa aka buga masa kamar yadda ya saba a kasashen ketare, to amma kudin suka bata bayan an shiga da su a kasar cikin shekarar da ta gabata.

Ministan yada labarai na kasar Eugene Nagbe, ya ce kudaden da suka bata adadinsu ya kai 5% na karfin tattalin arzikin kasar. 

Charles Sirleaf dan tsohuwar shugabar kasar, da kuma tsohon gwamnan babban bankin kasar Milton Weeks na daga cikin wadanda aka hana wa fita daga kasar domin bincike.