Isa ga babban shafi
Najeriya

Rashawa a Najeriya:Kotun Italiya ta daure masu laifi

Alkalin wata kotu da ke birnin Milan na kasar Italiya, ya yanke hukuncin farko a game da batun bayar da rashawa domin kamfanonin mai na Shell da kuma ENI damar sayen wata katafariyar rijiyar mai a tarayyar Najeriya.

Kamfanonin mai na Shell da Eni
Kamfanonin mai na Shell da Eni www.rfi.fr
Talla

Alkalin ya yanke hukuncin dauri na tsawon shekaru hurhudu a kan mutane biyu bayan da aka tabbatar da cewa su ne manyan dillalan da suka taka rawa wajen kulla wani ciniki da ya kai dala bilyan daya da milyan  300 a shekara ta 2011.

An bayyana cewa Emeka Obi dan Najeriya da kuma wani dan Italiya mai suna Gianluca Di Nardo, su ne manyan dillalan da suka yi hada hadar kulla cinikin, da ya bai wa kamfanonin biyu damar samun lasisin mallakar katafariyar rijiyar mai ta OPL-mai lamba 245.

Baya ga daurin shekaru hurhudu a gidan yari, kotun ta kuma kwace dala milyan 98,4 daga hannun dan Najeriyar, sai kuma kudin Suisse Francs milyan 21 mallakin dan kasar ta Italiya.

Masu shigar da kara a gaban kotun sun yi zargin cewa Mista Obi shugaban kamfanin mai na Energy Venture Partners, ya taka rawar dillancin ne a madadin tsohon ministan mai na Najeriya Dan Etete

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.