rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Nijar Chadi Kamaru Al Qaeda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan Boko Haram sun kashe mutane 9 a Najeriya

media
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM

‘Yan Boko Haram sun kashe mutane 9 tare da raunata wasu 9 a harin baya bayan nan da suka kai cikin jihar Borno da ke tarayyar Najeriya.


Wani mai suna Ibrahim Liman, jami’i a rundunar mayakan sa-kai da ake kira Kato da Gora, ya ce mayakan na Boko Haram sun kashe mutanen 9 ne a kauyukan Kalari Abdiye da kuma Amarwa wadanda ba su da nisa daga Maiduguri, yayin da suka raunata wasu mutane 9 na daban.

Lamarin ya faru ne a marecen jiya laraba, inda mayakan suka afka wa garin da misalin karfe 8 da rabi na dare lokacin da ake shatata ruwan sama.

Daga bisani mayakan na Boko Haram sun kona kauyukan biyu da ke cikin karamar hukumar mulkin Kondufga kurmus.