Isa ga babban shafi
Togo

Masu hamayya da juna a Togo sun cimma jituwa

Bangarori masu hamayya da juna a siyasar kasar Togo, sun ce an samu gagarumin cigaba a tattaunawar da ake yi karkashin inuwar kungiyar Ci gaban Tattalin Arzikin Afrika Ecowas, domin gudanar da zabubuka a kasar.

Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Togo  Jean-Pierre Fabre da shugaba Faure Gnassingbé.
Shugaban babbar jam'iyyar adawa ta Togo Jean-Pierre Fabre da shugaba Faure Gnassingbé. AFP . Issouf Sanogo
Talla

Bayan tattaunawar yini daya da aka yi a birnin Lome karkashin jagorancin manzannin kungiyar ta Ecowas ko Cedeao, ministan kwadagon kasar ta Togo wanda ke wakiltar bangaren gwamnati a tattaunawa Gilbert Bawara, ya ce bangarorin biyu sun cimma jituwa dangane da muhimman batutuwan da ke gabansu.

Bayan ganawar, bangaren adawa ya amince ya bayar da sunayen mutane 8 da za su wakilce shi a Hukumar zaben kasar, hukumar da za a kaddamar kafin ranar 30 ga wannan wata na Satumba.

Jean-Pierre Fabre, shugaban jam’iyyar adawa ta ANC, ya ce tabbas an warware sabani a game da wasu batutuwa musamman yadda hukumar zaben za ta gudanar da ayyukanta.

To sai dai akwai bututuwan da har yanzu ba a cimma matsaya ba tsakanin gwamantin Faure Gnasingbe da kuma ‘yan adawa, da suka hada da yi wa kundin tsarin mulki gyara don kayyade wa’adin shugabanci da tsayar da ranar zaben ‘yan majalisa kafin ranar 20 ga watan Disamba mai zuwa da dai sauransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.