rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Mali Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

'Yan bindiga sun bude wuta kan fararen hula a wani kauye dake Mali

media
Wasu dakaru dake aikin wanzar da zaman lafiya a Mali REUTERS/Benoit Tessier/File Photo

Wani Kazamin harin da yan bindiga suka kai kusa da iyakar Nijar dake Mali yayi sanadiyar hallaka fararen hula 12.


Sanarwar da kungiyar kare muradun yan Kabilar Azawad ta fitar yace an kai harin ne a yammacin garin Menaka, inda yan bindiga akan Babura suka bude wuta kan jama’a.

Rahotanni sun ce akalla mutane 200 akasari Fulani ne aka kashe a rikicin dake gudana tsakanin abzinawa da Fulani a yankin.

Gwamnatin kasar a kokarin ta na kawo karshen rikic a wadanan yankuna ta sanar da shirin aike tawaga zuwa Shugabannin kabilu na yankunan cikin dan karamin lokaci.