An ceto wasu bakin haure kusan 700
Kusan bakin haure 700 ne jami’an kula da gaban tukur kasar Spain suka samu kubutar da su daga salwancewa a teku a karshen makon nan.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun gwamnatin Spain ya sanar da cewa mutane 405 daga jirgin ruwa ‘yan kasada masu safarar bakin haure aka ceto su, kuma sun hada da jira-jirai da yara kanana 7 daga kasashen Africa.
Kasar Spain dai ta kasance babbar zango da bakin haure ke matukar son yada zango a kokarin kaiwa ga kasashen Turai neman sabuwar rayuwa.
A jiya lahadi jirgin ruwan Aquarius ya ceto wasu bakin haure 58 da aka garzaya da su zuwa tsibirin Malte.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu