rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ghana Amurka Malawi Kenya Masar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Melania Trump ta isa kasar Ghana

media
Matar Donald Trump, Melania Trump da matar shugaban Ghana Rebecca Akufo-Addo a filin jiragen sama na Accra, Ghana Oktoba 2, 2018. © AP

Matar shugaban Amurka Donald Trump ta isa birnin Accra na kasar Ghana a wannan talata, zangon farko a ziyarar da ta fara  a kasashe hudu na Afirka.


Dimbin jama’a ne a karkashin jagorancin matar shugaban kasar Ghana Rabecca Akufo-Addo suka tarbi Melania Trump lokacin da ta sauka a filin jiragen sama na Kotoka da ke birnin na Accra.

A lokacin wannan ziyara, bayan ganawa da matan shugabannin da za ta ziyarta, Melania za ta yi kokarin sanar da duniya wasu daga cikin muhimman ayyukan da hukumar Raya Kasashe ta Amurka USAID ke gudanarwar musamman a nahiyar ta Afirka.

Bayan kasar Ghana, matar shugaban na Amurka za ta kuma ziyarci kasashen Malawi, Kenya da kuma Masar karon farko tun lokacin  da mijinta ya dare shugabancin Amurka kusan shekaru biyu da suka gabata.