rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Kenya Ghana Masar Malawi Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Uwargidan Donald Trump na ziyara a kasashen Afrika

media
Uwargidan shugaban Amurka Melania Trump REUTERS/Carlos Barria

Uwargidan shugaban Amurka Donald Trump, wato Melania Trump na ziyara a wasu kasashen nahiyar Afrika da suka hada da Ghana da Malawi da Kenya da kuma Masar.


A karon farko kenan da Melania ke gudanar da irin wannan gagarumar ziyara ita kadai, yayin da mai magana da yawunta, Stephanie Grisham ta ce, ziyarar ta ta’allaka akan diflomasiya da kuma jin-kai ga kananan yara.

A makon jiya ne, mai gidanta Donald Trump ya sanar da shirin ziyarar Melania a Afrika, yayin da ya ce, shi da matarsa suna matukar kaunar nahiyar.

Trump ya bayyana Afrika a matsayin wata nahiya mai kayatarwa ta fuskoki da dama.

A can baya, shugaban ya bayyana Afrika a matsayin wani yanki mai cike da kazanta, lamarin da ya janyo masa suka daga bangarori da dama na nahiyar.