rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kenya Uhuru Kenyatta

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Jami'an Tsaro A Kenya Na Tsare Da "Yan Kasar China 5 Dake Barazana Ga Tsaro

media
Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya rfi

Jami'an tsaro a  Kenya na tsare da wasu ‘yan kasar China biyar da aka same su da wasu tarkacen naurori na tsaro da suka fara dasawa a kasar da cewa suna son kafa kamfanin harkokin tsaro ne, duk da cewa basu da takardun izinin shiga kasar.


Gwamnatin kasar na ta yada wannan kamu na ‘yan kasar China a wani lokaci da ake kukan yawaitan ‘yan China dake leburanci a Kenyan ganin akwai dimbin matasan Kenya marasa ayyukan yi.

Cikin kayayyaklin da aka samu a wajen su sun hada da kayan soja, wayoyin sadarwa na oba-oba, da kuma tulin gwangwanayen barkonun tsohuwa.

Yanzu haka ana tsare dasu kafin daukan mataki na gaba.