rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Paul Biya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An kawo karshen yakin neman zabe a Kamaru

media
Shugaban Kamaru Paul Biya. AFP

An kammala yakin neman zaben shugaban kasar Kamaru, wanda zai gudana a wannan Lahadi, inda shugaba mai ci Paul Biya zai fafata da wasu 'yan takara 8.


Wakilinmu Muhammad Salissou Hamissou, wanda yanzu haka yake birnin Yaounde ya aiko mana da rahoto akan halin da ake ciki.

An kawo karshen yakin neman zabe a Kamaru 06/10/2018 - Daga Salissou Hamissou Saurare

Kafin rufewa ko kammala yakin neman zaben shugbancin na Kamaru, biyu daga cikin manyan jami'yun siyasa a kasar, sun cimma yarjejeniyar marawa dan takara guda baya a zaben shugaban kasar da za’a yi a gobe Lahadi.

Jam’iyyun na FDP da MRC sun cimma yarjejeniyar ce, bayan da dan takarar FDP Akere Muna, ya amince da janye takararsa don marawa Maurice Kamto na MRC baya, domin kayarda shugaba mai ci Paul Biya, mai shekaru 85 dake neman zarcewa wa'adi na shida.

Hadin kan jam’iyyun adawar dai bai shafi, babbar jam’iyyar adawar kasar ta Kamaru ba wato Social Democratic Front, wadda Joshua Osih ke mata takara.