rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Kamaru Paul Biya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu tashin hankali a zaben Kamaru

media
An girke jami'an tsaro a yankin da shugaba Paul Biya ya kada kuri'arsa REUTERS/Zohra Bensemra

Rahotanni daga kamaru sun ce, an samu yan tashe-tahsen hankula a sassan kasar da ake fama da matsalar 'yan aware yayin gudanar da zaben shugaban kasa, in da  aka soke kuri’u a wasu wuraren saboda fargabar matsalar tsaro.


Rahotanni na cewa, jami’an tsaro sun harbe mutane uku da ake zargin cewa ‘yan aware ne daga Bamenda

Harbin na zuwa bayan zargin ‘yan awaren da kai farmaki kan jama’ar da ke kai–kawo a Bamenda, yayin da a ranar Juma’a ma  aka harbe wasu ‘yan awaren Ambazonia uku a birnin Buea.

Tuni aka rufe rumfunan zabe, in da a yanzu ake dakon sakamakon karshe da za a fitar a tsakanin kwanaki 15 kamar yadda dokar kasar ta tanada.

Ana kyautata zaton shugaba mai ci, Paul Biya mai shekaru 85 ya sake komawa kan kujerarsa.