rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar Armenia Sahel Ta'addanci Tafkin Chadi Majalisar Dinkin Duniya Libya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ta'addanci:Shugaba Issifou na neman taimakon kasashe

media
Shugaba Issifou Mahamadou na Nijar ONEP-NIGER

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mahamadou Issifou, wanda ke gabatar da jawabi wurin taron kasashe masu mu’amala da harshen Faransancin da ke gudana yanzu haka a kasar Armenia, ya bukaci kasashen duniya da su taimaka wa yankin Sahel da kuma sauran kasashen da ke zagayen tafkin Chadi, domin tunkarar matsalar tsaro da suke fama da ita.


Shugaban ya ce, "Ba za a taba samun ci gaba a yankin Francophonie ba sai tare da zaman lafiya da tsaro. A zahiri take cewa da dama daga cikin kasashen wannan kungiya na fama da ‘yan ta’adda da kuma kungiyoyin masu aikata miyagun laifufuka."

"Wannan matsala ce da kasashen yankin tafkin Chadi da kuma na Sahel ke fama da ita. Tabbas, wadannan kasashe sun samu tallafin sauran kasashen duniya ciki har da Francophonie." in ji shugaba Issifou.

Issifou ya kara da cewa, "kasashen Sahel sun kafa rundunar G5-Sahel, wadda ta samu amincewar Majalisar Dinkin Duniya, to amma rundunar na fatan samun tallafin kudi daga kasashen duniya, Wadanda suka haddasa rikicin da ake fama da shi a Libya wanda kuma ya yadu zuwa sauran kasashe, bai kamata su manta da yankin Sahel ba."