Kamaru
Kamaru mamba a hukumar kare hakkin dan adama ta duniya
An zabi kasashen Bahrein, Kamaru da Philippines a matsayin mambobin Hukumar Kare hakkin bil’adama ta MDD a daidai lokacin da ake zargin gwamnatocin kasashen da tauye hakkin dan adam.
Wallafawa ranar:
Talla
Hukumar, mai wakilai 47, kashi 1 cikin 3 na wakilanta ana zaben su ne domin yin wa’adi na shekaru uku, inda a halin yanzu Kamaru, Bahrein da kuma Philippines za su kasance mambobi daga 2021-2021.
Dukkanin kasashe 18 da suka nemi wannan matsayi sun yi nasara bayan kada kuri’ar lokacin zaman da hukumar ta yi a birnin Geneva ranar juma’ar da ta gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu