rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM ISIL Al Qaeda

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sojojin Najeriya 2 sun mutu a Arewa maso gabashin kasar

media
Sojojin Najeriya a garin Maïduguri 14 ga watan mayun 2015. REUTERS/Stringer

Sojojin Najeriya biyu ne suka mutu yayin da wasu 9 suka samu raunuka sakamakon taka nakiya da aka binne a yankin arewa maso gabashin kasar mai fama da ‘yan Boko Haram.


Bayanai sun ce hatsarin farko ya faru ne a kusa da kauyen Kumshe wanda ba ya da nisa da iyakar kasar da Kamaru.

Fashwa ta biyu kuwa ta faru ne  a kan hanyar da ke sada garin Dikwa da Marte a cewar wadanda suka shaidi lamarin.