Isa ga babban shafi
Sudan

Tsohon shugaban Sudan Al-Dahab ya rasu yana da shekaru 83

Tsohon shugaban kasar Sudan Abdulrahman Al-Dahab ya rasu a Riyadh babban birnin Saudi Arabia yau Alhamis yana da shekaru 83 a duniya.

Abdulrahman Al-Dahab ya rike mukamin ministan tsaron Sudan a shekarar 1984 zamanin mulkin shugaba Gaafar.
Abdulrahman Al-Dahab ya rike mukamin ministan tsaron Sudan a shekarar 1984 zamanin mulkin shugaba Gaafar. Reuters
Talla

Al-Dahab wanda shi ne shugaban Sudan na 5 kafar Talabijin ta Al Arabiya mallakin kasar Saudi Arabia da ta fitar da labarin bata sanar da musabbabin mutuwar ta sa ba.

Abdulrahman Al-Dalab wanda tsohon jami’in soja ne ya shugabanci dunkulalliyar kasar ta Sudan ne daga ranar 6 ga watan Aprilun 1985 zuwa 6 ga watan Mayun 1986.

Tsohon shugaban wanda fitacce ne a kasar ta Sudan tauraruwarsa ta haskaka ne bayan nadin da tsohon shugaba Gaafar Nimeiry ya yi masa a matsayin ministan tsaron kasar a shekarar 1984.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.