rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Burkina Faso Cote d'Ivoire

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa zata ci gaba da dafawa dangane da tsaro a Sahel

media
Jean Yves Ledrian Ministan harakokin wajen Faransa

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ziyarci birnin Ouagadougou na kasar Burkina Faso a jiya alhamis, inda ya tattauna da shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore dangane da batun tsaro.


Burkina Faso da wasu kasashen yankin Sahel na fuskantar matsantan hare-hare a cikin ‘yan watannin baya-bayan nan musamman bangaren iyakar Burkina Faso da Mali, lamarin da ya sa dakarun rundunar Barkhane da Faransa ta girke domin fada da ayyukan ta’addanci a yankin shirya kai dauki ga kasar.

A jiya Jean Yves Ledrian Ministan harkokin wajen Faransa, ya ziyarci birnin Abidjan na kasar Cote d’Ivoire inda Faransa ke shirin gina wata makarantar horas da jami’an tsaro dubarun yaki da ayyukan ta’addanci.

Tun cikin shekarar bara ne ta sanar da shirin gina wannan makaranta a Jacqueville mai tazarar kilomita 50 daga birnin Abidjan.