Isa ga babban shafi
Benin

Kotu ta daure jagoran 'yan adawa a Benin

Kotu a Jamhuriyar Benin ta yanke wa jagoran ‘yan adawar kasar kuma hamshakin dan kasuwar kasar Sebastien Ajavon hukuncin daurin shekaru 20 bayan samunsa da laifin fataucin miyagun kwayoyi duk da cewa ya gudu ya bar kasar.

Sébastien Ajavon,Shugaban kungiyar yan kasuwa ta Jamhuriyar Benin
Sébastien Ajavon,Shugaban kungiyar yan kasuwa ta Jamhuriyar Benin CHARLES PLACIDE / AFP
Talla

Ajavon wanda ya taimaka wa shugaban kasar mai ci Patrice Talon domin samun nasara a zaben 2016, kotun wanda ta yi zamanta a birnin Porto Novo dake babban birnin kasar ta fitar da sammacin kasa da kasa domin taso keyarsa zuwa gida daga Faransa inda yake zaune yanzu haka.

Da dama daga cikin yan siyasa a kasar suka soma bayyana damuwa tareda yin tir da Allah wadai zuwa hukumomin kasar ta Benin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.