Isa ga babban shafi
Kamaru

An yi awon gaba da kanwar John Fru Ndi

Wasu da ake zargin yan aware a Kamaru sun kai hari tare da yin awon gaba da kanwar dan adawa John Fru Ndi, kana suka kone gidan shi.

John Fru Ndi daga yankin yan aware na kasar Kamaru
John Fru Ndi daga yankin yan aware na kasar Kamaru rfi hausa
Talla

Wannan dai karo na biyu kenan da ake kai wa john Fru Ndi hari saboda zargin da ake masa a matsayin mai zubar da mutuncin mutanen yankin.

A makon da ya gabata ne Shugaban gungun lauyoyin masu kare shuwagabanin yankin yan aware dake amfani da turancin Inglishi, John Fru Nsoh ya sanar da kamfanin dillancin labaran Afp cewa, an kama Ayuk Tabe ne ba a kan ka’ida ba a Najeriya, kuma aka dauko shi a cikin mummunan yanayi, ta hanyar sanyo shi a jirgin sama ba tare da damarar da ta daure shi a kujerar jirgin ba.

Su dai gungun lauyoyin, sun shigar da korafin nasu ne a gaban kotun daukaka kara da ke Yaounde babban birnin kasar ta Kamaru, inda suke fatan a salami Ayuk Tabe da sauran shuwagabanin yankin yan awaren ta hanyar bayyana su a matsayin marasa laifi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.