Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Boko Haram ta hallaka manoma 12 a jihar Borno ta Najeriya

Mayakan kungiyar boko haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya sun hallaka manoma 12 a kauyen Kalle da ke wajen birnin Maiduguri na jihar Borno ta hanyar yi musu yankan rago da wuka.

Wani manomi cikin mutane 3 da suka tsira da rayukansu a harin na yau, ya ce lokacin da suka ji tsayawar motocin mayakan ne kowannensu ya ranta ana kare amma suka bisu suka kamo su.
Wani manomi cikin mutane 3 da suka tsira da rayukansu a harin na yau, ya ce lokacin da suka ji tsayawar motocin mayakan ne kowannensu ya ranta ana kare amma suka bisu suka kamo su. REUTERS/Emmanuel Braun
Talla

Rahotanni sun ce mayakan sun isa kauyen na Kalle ne mai nisan kilomita 17 da birnin Maiduguri yau Asabar lokacin da manoman ket saka da aikinsu na gona.

Wani manomi cikin mutane 3 da suka tsira da rayukansu a harin na yau, ya ce lokacin da suka ji tsayawar motocin mayakan ne kowannensu ya ranta ana kare amma suka bisu suka kamo su.

Kawo yanzu dai ba a tabbatar da wanne tsagi ne daga kungiyar ta Boko Haram ya kai harin na yau ba, ko da dai ana ganin mayakan kungiyar masu biyayya ga Abubakar Shekau sun yi kaurin suna wajen kai hare-haren kisa kan fararen hula sabanin wadanda ke biyayya ga kungiyar IS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.