rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Taron baje kolin kamfanonin yada labarai

media
kafafen yada labarai da dama sun halarci taron Abuja REUTERS/Charles Platiau

A jiya ne aka bude bikin baje kolin kamfanonin yada labarai wanda hukumar kula da kafafen yada labaran Najeriya wato NBC ta shirya a Abuja Najeriya.Taron ya samu halartar shugabanin kafafen yada labaran Najeriya da masana harakokin jarida ciki da wajen kasar.


An shirya taron baje kolin ne a kokarin hukumar na yunkurin kamo manyan kasashen Duniya da suka ci gaba ta fannin yin amfanin da sabbin na’urorin ayyukan yada labarai na zamani.

Taron zai baiwa masana damar tattaunawa dama duba wasu hanyoyin magance matsallolin da ake fuskanta a duniyar Kamfanonin yada labarai a Najeriya.bikin baje kolin kafafen yada labarai na da nufin daidaita al’amuran yada labarai da kuma kamun kafa da manyan kasashe Duniya.