rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tasirin kwace makamai daga yan tawaye a Bangui

media
Daya daga cikin yan tawayen Afrika ta tsakiya FLORENT VERGNES/AFP

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ya zuwa karshen wannan shekarar, jamhuriyar Afrika ta Tsakiya zata fara kwace makamai a hannun mayakan sa kai daban-daban a kasar.


Manzon majalisar dinkin Duniya Parfait Onanga-Anyanga, ya shaida hakan a zauren taron kwamitin sulhun majalisar ta dinkin Duniya, inda ya ce tuni aka yi nisa kan hanyoyin samar da zaman lafiya a kasar ta Afrika ta Tsakiya, tun lokacin da dakarun wanzar da zaman lafiyar Majalisar suka isa kasar a shekarar 2014.