rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Habasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Habasha ta nada mace ta farko a kujerar shugaban kasa

media
Sahle-Work Zewde, sabuwar shugabar kasar Habasha UN

A karon farko Habasaha ta nada mace a matsayin shugabar kasa, bayan murabus din shugaba Mulutu Teshome daga wannan mukami.


A wata kuri’ar hadin-kai da suka kada, ‘Yan Majalisar Dokokin Habasha sun zabi Sahle-Work Zewde mai shekaru 68 don maye gurbin Teshome da ya yi murabus cikin wani yanayi mai sarkakiya.

Nadin sabuwar shugabar na zuwa bayan mako guda da Firaministan Kasar mai fafutukar kawo sauyi, Abiy Mohammed ya nada mata da dama a Majalisar Ministocinsa.

Sabuwar shugabar ta ce, muddin aka ci gaba da samun irin wannan sauyi a kasar wadda ita ce ta biyu a wayan al’umma a Afrika, to babu shakka kasar za ta ci gaba har ta magance matsalolin banbance- banbancen addini da kabilanci.

An haifi Uwargida Sahle-Work, a birnin Addis Ababa, sannan ta yi karatu a wata jami’a da ke Faransa kafin daga bisani ta zama jakadiyar Habasha a Faransa da Djibouti da Senegal.

Kazalika ta rike babban mukami a Kungiyar Kasashen Afrika ta AU, sannan kuma kwararriya ce a harsunan Turancin Ingilishi da Faransanci har ma da yaran Amharic da ya kasance babban harshe a Habasha.

Ana saran Sahle-Work ta shafe tsawon wa’adi biyu na shekaru shida-shida akan wannan mukami na shugabar kasa.