rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kungiyar Kwadago a Najeriya za ta tsunduma yajin aiki mafi muni

media
Shugaban kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC Ayuba Philibus Wabba yayin jagorantar tattakin 'ya'yan kungiyar kwadago a garin Abuja. REUTERS/Afolabi Sotunde

Kungiyar kwadago a Najeriya ta bukaci al’ummar kasar su tanadi abinci da za su yi amfani da shi na tsawon lokaci la’akari da yadda za su dakatar da kowacce hada-hada a fadin kasar matukar suka tsunduma sabon yajin aikin da su ke shirin farawa a wata mai kamawa.


Cikin wata takaddar bayan taro da kungiyar ta NLC ta fitar ta sanar da cewa ta cimma matsayar sake tsunduma yajin aikin bayan taro da shugabanninta na sassan Najeriyar a cikin makon nan.

Takardar bayan taron dauke da sa hannun shugaban kungiyar Kwadagon na kasa Ayuba Wabba tare da babban sakataren ta Dr Peter Ozo-Eson ta ce kungiyar za ta tsunduma yajin aikin ranar 6 ga watan Nuwamba mai kamawa.

cewar Wabba, salon yajin aikin na wannan karon ya sha bam bam da wanda aka saba gani domin kuwa za su kulle ilahirin kamfanoni da ma’aikatu da sassan gwamnati da ma masu zaman kansu.