rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya Kaduna

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dokar takaita zirga-zirga ta dawo sabuwa a Kaduna

media
Dawo da dokar ta biyo bayan jita-jitar rikici a wasu sassa na jihar. Reuters

Gwamnatin Kaduna a yankin arewacin Najeriya ta sake maido da dokar takaita zirga ziraga tsawon sa'o'i 24 a ciki da kewayen jihar, wadda ta sassauta a Lahadin da ta gabata.


Matakin ya biyo bayan zaman dar-dar da jama’a suka sake fuskanta, bayan gano gawar Sarkin Kadara, mai rike da sarautar Agamo Adara, Maiwada Galadima, wanda aka sace a Juma’ar makon da ya gabata.

Dawo da Dokar dai na zuwa ne kwanaki hudu bayan sassauta dokar wadda aka sanya sakamakon wani tashin hankali da ya kai ga mutuwar mutane 55 a kasuwar magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar ta Kaduna.

Kaduna dai na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fuskantar matsalolin tsaro masu alaka da satar mutane don neman kudin fansa rikicin kabilu dama na addini.