Isa ga babban shafi
Kamaru

Vamulke zai sake gurfana a gaban kotun Kamaru

A ranar Laraba ake saran Amadu Vamulke, tsohon shugaban kafar yada labaran kasar Kamaru, CRTV, ya sake gurfana a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta musamman a Yaounde, babban birnin kasar, karo na 13, bisa zargin cin hanci da rashawa.

Amadou Vamulke
Amadou Vamulke cameroon-info.net
Talla

Vamulke, wanda dan jarida ne, kuma tsohon shugaban gidan rediyo da talabijin din kasar Kamaru, ya share sama da shekaru biyu yana tsare a gidan kurkukun Kondengi a birnin Yaounde.

Mahukuntan Kamaru  na zargin Vamulke da ruf da ciki da kudin ma’aikatarsa da ya kai sama da biliyan uku na kudin Cefa, zargin da ya musanta, amma masana harkokin shari’a da dama suka amince da shi, ganin cewa ya halarci zaman kotu har sau 13 cikin shekaru biyu ba tare da gwamnati ta tabbatar da wata shaida ko hujja da ke tabbatar da zargin ba.

Gamayyar Kungiyoyin Kare Hakkin ‘Yan jaridu da na Kare Hakkin Bil’adama daga ciki da wajen kasar, karkashin jagorancin tsohon shugaban gidan rediyon Faransa, Alain Maze, na fatan ganin an sallame shi, in da suke dangata ci gaba da tsare shi da siyasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.