rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An samu barkewar cutar Kwalara a jihar Gombe ta Najeriya

media
A baya-bayan nan dai ana ci gaba da fuskantar barkewar cutar ta Kwalara a sassan Najeriya. REUTERS/Philimon Bulawayo

Hukumomin Lafiya a jihar Gombe da ke Tarayyar Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla Mutane 5 yayinda wasu 16 kuma yanzu haka ke karbar kulawa a Asibiti sakamakon barkewar cutar Kwalara a wasu sassa na jihar.


Dr Nuhu Bile wanda ke matsayin mukaddashin shugaban sashen kula da cutuka masu saurin yaduwa na jihar ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa tun a cikin watan Octoba aka fara samun wadanda suka kamu da cutar ta Kwalara.

Dr Bile ya ce cutar ta fi tsananta ne a yankin Kembu na karamar hukumar Balanga da ke jihar yayinda yanzu haka marasa lafiyan ke ci gaba da karbar kulawar gaggawa don ceto rayukansu.

A cewarsa a aikin hadin gwiwar da suka gudanar da hukumar lafiya ta duniya WHO a yankin da aka samu bullar cutar sun yi nasarar magance cutar kan mutane akalla 70 yayinda wasu daga ciki suka mutu tun a watan Oktoba.