rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Sudan ta Kudu Tarayyar Afrika

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Sudan Ta Kudu Ya Saki Manyan 'Yan Tawaye Da Ke Tsare

media
Shugaba Salva Kiir tare da madugun adawa Riek Machar ranar 12 ga watan Satumba 2018. rfi

Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu ta saki wasu manya na hannun daman madugun ‘yan tawayen kasar Reik Machar da ake tsare dasu a gidan Kaso, domin cika wasu sharuddan dake kunshe cikin yarjejeniyar sulhu da bangarorin dake yaki a kasar suka sanya hannu.


Mutane biyu daga ciki sun hada da wani tsohon sojan Africa ta Kudu da yayi ritaya William Endley wanda mashawarcin madugun adawan ne, sai kuma James Gatdet kakakin bangaren ‘yan tawayen wadanda  aka zartas masu da hukuncin kisa a chan baya.

Tun ranar laraba ne dai shugaban kasar Salva Kiir ya umarci a saki mutanen saboda cika sharuddan yarjejeniyar sulhu da aka kulla.

Mutane akalla dubu 383 aka kashe a yakin kasar da aka fara tun shekara ta 2013.