rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Akwai alamun fuskantar karancin man fetur a Najeriya

media
Masana tattalin arziki dai na ganin tsunduma yajin aikin na ranar 6 ga watan Nuwamba zai taka muhimmiyar rawa wajen kassara tattalin arzikin kasar da bai jima da dawowa hayyacinsa ba. rfi hausa

Akwai yiwuwar a fuskanci karancin man fetur a sassan Najeriya bayan da hadakar Kungiyar ma’aikatan bangaren man fetur da Iskar gas NUPENG ta sanar da aniyarta ta mara baya ga kungiyar kwadagon kasar NLC wajen tsunduma yajin aiki a ranar 6 ga watan Nuwamban da muke ciki.


A cewar kungiyar za ta bi sahun NLC wajen tsunduma yajin aikin na ranar Talata tare da dakatar da duk wasu al'amuranta na jigilar mai a sassan kasar. 

A juma’ar da ta gabata ne gwamnatin Najeriyar ta karbi wani hukuncin Kotu da ya haramtawa kungiyoyin kwadagon kasar NLC da TUC tsunduma yajin aikin kamar yadda suka tsara ko da dai ilahirin kungiyoyin sun yi watsi da hukuncin kotun bisa cewa dama ba tare da yardar kotun suke gudanar da al’amuransu ba.

Masana tattalin arziki dai na ganin tsunduma yajin aikin na ranar 6 ga watan Nuwamba zai taka muhimmiyar rawa wajen kassara tattalin arzikin kasar da bai jima da dawowa hayyacinsa ba.

Ka zalika kungiyoyin kwadagon su bukaci al'ummar Najeriya su yi tanadin kayakin bukaci don kaucewa shiga matsala a tsawon lokacin da za su dauka suna gudanar da yajin aikin wanda za su hana bude hatta kasuwanni.