rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Eritrea Habasha Hakkin Dan Adam Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kwamitin tsaron MDD zai dagewa Eritrea takunkumai

media
Zauren Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya. AFP/File

Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya, ya soma shirin dagewa Eritrea takunkuman da aka kakaba mata, biyo bayan amincewar Amurka dangane da daukar matakin, wadda a baya ke neman tasawaita su, duk da yarjejeniya sulhun da kasar ta Eritrea ta cimma da Habasha.


Birtaniya ce ta gabatar da kudurin neman dagewa Eritrea takunkuman da suka hada da, haramta mata sayen makamai, kwace kadarorin kasar dake kasashen waje, da kuma haramtawa wasu manyan jami’an kasar tafiye-tafiye.

Kwamitin tsaron majalisar dinkin duniyar, ya tsayar da 14 ga watan Nuwamba da muke ciki, a matsayin ranar da za’a kada kuri’a kan bukatar dage takunkuman.

A watan Yuli Eritrea da Habasha suka cimma yarjejeniyar kawo karshen rikicin dake tsakaninsu na kan iyaka, sai dai tun a waccan lokacin, Amurka, tare da goyon bayan Faransa da Birtaniya, suka dage cewa, tilas, kasar ta nuna da gaske take a bangaren mutunta hakkin dan adam kafin a dage takunkuman da aka kakaba mata.