Bakonmu a Yau
Alhaji Ali Madugu mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu a Najeriya kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya a Afrika
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:41
Gwamnatin Najeriya ta kafa wani kwamiti na musamman domin sake nazari kan bukatar kasar na sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwancin bai daya na kasashen Afirka.A karshen makon kwamitin ya gudana da wani taro tsakanin sa da masu ruwa da tsakani kan harkokin kasuwancin, wanda ya samu halartar mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo.Bayan taron mun tattauna da Alhaji Ali Madugu, mataimakin shugaban kungiyar masu masana’antu a Najeriya, kuma ga bayanin da yayi mana kan makasudin taron.