rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Afrika Sahel Senegal

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An bude taron masana harkokin tsaro na Afrika a Senegal

media
Minister tsaron Faransa Florence Parly da ke halartar taron, ta ce ya zuwa yanzu kashi daya bisa hudu ne kawai na euro miliyan 400 da aka yi alkawarin tallafawa rundunar domin gudanar da ayyukan ta su ka samu. RFI/Olivier Fourt

Yau ake bude taron masana harkokin tsaro na Afrika can a kasar Senegal, a dai dai lokacin da ake ci gaba da bayyana damuwa kan makomar rundunar dakarun G5 Sahel da ke fama da matsalar kudin aiki.


Taron wanda ake saran zai tattauna batutuwa da dama da suka hada da yaki da ta’addanci da kwararar baki zuwa Turai da kuma nasarar da ake samu kan Yan ta’adda, zai kuma yi nazari kan matsalar kudin da ta dabaibaye rundunar G5 Sahel wadda aka kafa musamman don fuskantar duk wani kalubale daga Yan Ta’adda a Yankin Afirka ta Yamma.

Minister tsaron Faransa Florence Parly da ke halartar taron, ta ce ya zuwa yanzu kashi daya bisa hudu ne kawai na euro miliyan 400 da aka yi alkawarin tallafawa rundunar domin gudanar da ayyukan ta su ka samu.

Ita dai wannan runduna da ke samun goyan bayan Faransa, na da dakaru 5,000 da suka fito daga kasashen Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da kuma Nijar.

A watan Fabarairu, kasashen duniya sun yi alkawarin taimakawa rundunar da euro miliyan 420, cikin su harda Saudi Arabia da ta yi alkawarin ba da euro miliyan 100.