rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan ta'adda na kokarin kafa sansanoni yankin yammacin jamhuriyar Nijer

media
Sojojin jamhuriyar Nijar na kan aikin fada da yan ta'adda rfi-Hausa

Yankin Tilaberi dake yammacin kasar jamhuriyar Nijar na fuskantar barazanar kafuwar sansanonin kungiyoyin yan ta’adda da ke ikrarin jihadi, da suka fito daga kasashen Burkina Faso da Mali dake makwabtaka da kasar.


Har kawo yanzu dai, babu wani sansanin yan ta’adda a jamhuriyar Nijer, sai dai kuma yankin Tilaberi dake makwabtaka da kan iyakokin 3 na fuskantar barazanar zama sansanin yan ta’adda nan gaba

Yankin yanzu haka ya fara zama wata tinga ga kungiyoyin ‘yan ta’addan, kamar yadda Janar Ahmed Mohamed, shugaban rundunar sojan kasar ya sanar a wani taron gungun kasashen G5 Sahel da ya gudana a birnin Yamai.

Gungun kasashen G5-Sahel, dai da ya hada Burkina Faso, Mali, Niajar, Mauritaniya da kuma Tchadi, wata hadakar dakarun sojojin kasashen ne, domin yaki da kungiyoyin dake ikararin jihadi a yankin Sahel

Dan majalisar dokokin jahar ta Tilaberi Sumana Hasan ya ce, watanni 2 kenan da suka gabata suke suskantar wannan barazana daga yan ta’adda dake yawo a kan Babura a yankin, suna tilasta mutane kauyuka biyan Zakka, daya daga cikin shika shikai 5 da addinin musulunci ya kafu a kai.

Har ila yau yan ta’addan na kashe wadanda suka ki bin umarninsu tare da tilastawa jama’ar sauraren wazin su, yanzu haka dai gwamnati ta tura Karin dakaru a yankin domin fafatakar yan tsageran.