rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rahotanni Najeriya Muhalli Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari ya bukaci dakile dabi'ar yin bayan-gida a bainar jama'a

media
Buharin ya kuma bayyana damuwa kan yadda adadin mutanen da ke samun tsaftacaccen ruwan sha ya ragu daga kashi 32 a shekarar 1990 zuwa kashi 7 kacal a shekarar 2015. REUTERS/Afolabi Sotunde

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci kawo karshen yin bayan gida a bainar jama'a, domin tabbatar da tsaftar jama’a da kuma kare lafiyar su.


Yayin kaddamar da dokar ta baci kan samar da tsaftacaccen ruwan sha da kuma tsaftar muhalli, shugaban ya ce abin takaici ne yadda Najeriya ta zama kasa ta biyu da aka fi samun wannan matsala a duniya.

Shugaba Muhammadu Buhari da ya bayyana matsalar samun tsaftacaccen ruwan sha da tsaftar muhalli a matsayin manyan matsalolin da ke haifar da cututtuka a cikin al’umma, ya ce abin takaici ne yadda Najeriya ta zama kasa ta biyu a jerin kasashen duniya da ke fama da wannan matsala, ganin yadda kashi 25 na al’ummar kasar ke bayan gida a bainar jama’a.

Buharin ya kuma bayyana damuwa kan yadda adadin mutanen da ke samun tsaftacaccen ruwan sha ya ragu daga kashi 32 a shekarar 1990 zuwa kashi 7 kacal a shekarar 2015, kamar yadda tsaftar muhalli ya ragu da kashi 38.

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatoci a matakai daban daban ba sa bai wa harkar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli kular da ta dace da ita, saboda haka daga yanzu gwamnatocin jihohi za su dinga samun tallafi daga gwamnatin tarayya ne kawai idan sun aiwatar da shirin, wanda ake saran ya taimaka wajen kauda bayan gida a fili nan da shekarar 2025.