rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Majalisar Dinkin Duniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsakiyar Afrika na cikin barazanar matsananciyar yunwa

media
Wasu kananan yara da yaki ya raba da gidajensu a Afrika ta Tsakiya REUTERS/Siegfried Modola

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa, Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya mai fama da tashin hankali, na fuskantar barazanar yunwar da ba a taba ganin irinta ba a cikin shekaru 4 da suka gabata.


Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi wannan gargadi in da take cewa akalla mutane kusan miliyan biyu ke bukatar agajin abinci cikin gaggawa.

Mai Magana da Yawun Hukumar, Herve Verhoosel, ya ce alkaluman da suka tattara a watan Satumba, sun nuna cewar mutane miliyan guda da dubu 900 ke fama da karancin abinci mai gina jiki, tun bayan barkewar yaki a kasar a shekarar 2014.

Jami’in ya ce, daga cikin mutane dubu 620 da yakin ya raba da gidajensu, 6 daga cikin kowanne mutun 10 na zama ne da 'yan uwansu, wanda haka ke bayyana irin kalubalen da suke fuskanta.

Kasar Jamhuriyar Afrika ta tsakiya mai arzikin zinare da lu’u lu’u, ta fada cikin tahsin hankali tun daga shekarar 2013 da aka kifar da gwamnatin shugaba Francois Bozize, matakin da ya haifar da tashin hankalin tsakanin Musulmi da Kirista.