rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Muhammadu Buhari Najeriya Faransa Emmanuel Macron

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Buhari na halartar taron zaman lafiya na Paris a Faransa

media
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron. RFI hausa

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bar Abuja yau Juma’a don halartar taron zaman lafiya na birnin Paris da ke gudana can a Faransa karkashin jagorancin takwaransa Emmanuel Macron da zai fara gudana ranar Lahadi.


Taron wanda na hadin gwiwa ne tsakanin shugaban Faransa Emmanuel Macron da kungiyoyi masu zaman kansu, na da nufin neman hadin gwiwar kasashen duniya wajen wanzar da zaman lafiya mai dorewa tare da kawo karshen kalubalen da duniya ke fuskanta.

Muhammadu Buhari zai bi sahun magatakaddar Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteress da wasu shugabannin kasashen duniya wajen gabatar da jawabi a gaban taron don bayar da gudunmawa kan yadda za ca shawo kan kalubalen rashin zaman lafiya a sassan duniya.

Yayin taron shugaban na Najeriya zai kuma shiga sahun kasashen duniya da za su halarci bikin cika shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na daya.

During his visit to Paris, President Buhari will attend a luncheon hosted by President Emmanuel Macron of France in honour of visiting heads of delegations.

Ka zalika Muhammadu Buhari da tawagarsa za kuma su gana da al’ummar Najeriya mazauna Faransa.