Isa ga babban shafi
Habasha

'Yan sanda sun tono gawarwaki 200 daga kabari guda a Somali

‘Yan sandan Habasha sun tuno akalla gawarwakin mutane 200 daga cikin wani babban kabari da suka gano a tsakanin lardunan Oromia da Somali, dake yankin gabashin kasar.

Wani sashi na kabarin da masu binciken laifukan cin zarafin dan adam suka gano a lardin Somali na kasar Habasha, dauke da gawarwaki akalla 200..
Wani sashi na kabarin da masu binciken laifukan cin zarafin dan adam suka gano a lardin Somali na kasar Habasha, dauke da gawarwaki akalla 200.. Anadolu Agency
Talla

Kafafen yada labaran kasar ta Habasha sun rawaito cewa an gano kabarin ne a ranar Alhamis da ta gabata, yayin gudanar da bincike kan zargin aikata laifukan cin zarafin dan adam da ake yiwa wata rudunar sa kai mai biyayya ga tsohon shugaban lardin Somali Abdi Muhammad Omer.

A ranar 6 ga watan Agustan da ya gabata, aka tilastawa Abdi Omer yin murabus daga shugabancin lardin na Somali, daga bisani kuma, jami’an tsaro suka kama shi, sakamakon barkewar kazamin rikici a Jigjiga, babban birnin lardin.

A halin yanzu tsohon shugaban yana tsare, inda yake fuskantar shari’a kan zarginsa da aikata laifukan cin zarafin dan adam.

Yankin gabashin Habasha dai ya shafe shekaru masu yawa yana fama da rikici, a dalilin kokarin da sojin kasar ke yi na murkushe ‘yan tawayen Ogaden National Liberation Front ONLF, dake neman ballewa daga kasar.

Sai dai a watan Satumban da ya gabata, bangarorin biyu suka rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu.

Kafin cimma sulhun dai, kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch, ta dade tana bayyana cewa tsohon shugaban lardin Somali Abdi Omer yana tsare da wasu mayakan kungiyar ONLF a wani kurkukun sirri, inda ake azabtar da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.