Isa ga babban shafi
Gabon

Shugaba Ali Bango na fama da matsananciyar rashin lafiya

Wata majiya daga Fadar shugaban kasar Gabon Ali Bango na cewa shugaban na cikin matsananciyar rashin lafiya yanzu haka, yayinda ya ke ci gaba da jinya can a kasar Saudi Arabia.

A shekarar 2016 al’ummar kasar ta Gabon sun sake zaben Bongo don ci gaba da jan ragamar kasar.
A shekarar 2016 al’ummar kasar ta Gabon sun sake zaben Bongo don ci gaba da jan ragamar kasar. DR
Talla

Shugaban na Gabon mai shekaru 59 a ranar 24 ga watan Oktoba ne aka dauke shi ranga-ranga zuwa wani Asibiti da ke kasar Saudi Arabia, wanda ya kai ga jita-jitar mutuwarsa.

Mai magana da yawun fadar shugaban Ike Ngouoni ya ce yanzu haka shugaban na ci gaba da samun sauki.

Sai dai mai dakin Ali Bongo haifaffiyar Faransa Sylvia Bongo ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, shugaban ya gamu da mutuwar barin jiki ne.

Bongo ya rike mukamin ministan tsaro da kuma na harkokin wajen kasar yayin mulkin mahaifinsa Omar Bongo wanda ya rasu a shekarar 2009 lokacin da ya ket saka da mulki, kafin daga bisani a zabi Ali Bongo a matsayin wanda zai gaje shi.

Ka zalika a shekarar 2016 al’ummar kasar ta Gabon sun sake zaben Bongo don ci gaba da jan ragamar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.