Isa ga babban shafi
Tanzania

Shugaba Magufuli ya kori ministocinsa 2

Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya kori ministocinsa na ayyukan gona da na masana’antu da kasuwanci.

Ma'aikata a wata cibiyar sarrafa kwallon Cashew dake garin Bouake a kasar Ivory Coast. 23/02/2012.
Ma'aikata a wata cibiyar sarrafa kwallon Cashew dake garin Bouake a kasar Ivory Coast. 23/02/2012. REUTERS/ Thierry Gouegnon/Files
Talla

Magufuli ya dauki matakin ne domin kawo karshen takkadamar da ke barazanar yiwa tattalin arzikin kasar illa, inda manoman Cashew suka shafe makwanni bisa hawa kujerar nakin saida amfanin gonar ga ‘yan kasuwa a dalilin taya kayan nasu bisa farashi maras daraja da manoman suka ce ‘yan kasuwar na yi.

A halin da ake ciki shugaba Magufuli ya baiwa ‘yan kasuwa wa’adin zuwa gobe litinin da su saye kwallyen na Cashew daga manoman akan karin farashin dala 1 da kusan rabi da gwamntati ta amince da shi kan kowane ma’aunin kilo guda.

Fitar da kwallon Cashew kasashen ketare na taka muhimmiyar rawa wajen karfafa tattalin arzikin Tanzania ta fuskar samun kudaden waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.