Isa ga babban shafi
Kamaru

Iyayen dalibai a Kamaru sun nuna damuwa

A Kamaru iyayen yaran makaranta 80 da yan bindiga suka sace a makon jiya, sun bayyana fargabar su wajen kaucewa abinda ya faru da daliban makarantar Chibok dake Najeriya.

Wasu daga cikin yan kato da gora a kauyen Kamaru
Wasu daga cikin yan kato da gora a kauyen Kamaru Reinnier KAZE / AFP
Talla

Bayan mika musu ya’an nasu da aka sako, wasu daga cikin iyayen sun ce lokacin da aka sace yaran, sun yi tunanin cewar watakila ba zasu sake ganin su ba.

Issa Tchiroma Bakari ya ce, dukkanin dadiban 80 an sallamo su, sai dai bai bayyana cikin irin yanayin da aka sako yaran a ciki ba.

Yaran  dai dalibai ne a makarantar Presbyterian Secondary School dake Bamenda  babban birnin yankin arewa maso yammacin kasar Kamaru , an kuma sace su ne tare da wasu malamansu guda 3

Sai dai ministan Bakary yace a halin yanzu ba ya da wata masaniya dangane da halin da malaman uku ke ciki

Idan dai ba’a manta ba, a shekarar 2014 mayakan kungiyar boko haram sun sace dalibai mata daga makarantar Chibok 220, inda har ya zuwa yanzu wasu yaran basu koma gida ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.