Atiku na nazarin bai wa Naija Delta damar mamaye dukiyar man yankin
Dan takarar shugabancin kasa a Najeriya a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce yana tunanin bai wa Yankin Naija Delta izinin mallakar daukacin dukiyar man da ake hakowa sabanin kashi 13 da ake basu.
Wallafawa ranar:
A wata hirar da yayi da ‘The Africa Report’ da aka wallafa ranar laraba, Abubakar yace bashi da wata damuwa barin yankin ya mallaki dukiyar da yake da shi, sai dai kawai zai dorawa yankin harajin da zai dinga biya ga gwamnatin tarayya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana takaicin sa da yadda ake baiwa yankin kashi 13 kacal na arzikin man da ake sayarwa, yayinda a Jamhuriya ta farko kashi 50 ake basu.
Sai dai yace bukatar sa ba za ta samu ba dole sai an sake fasalin dokokin kasar ta hanyar lalama da kuma tattaunawa da sauran jama’a.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu